IQNA

Intifadar Falatinawa Kan Kudirin Trump Mutum 100 Sun Jikkata

23:15 - December 08, 2017
Lambar Labari: 3482179
Bangaen kasa da kasa, Taho mu gama mai tsanani da ya barke a tsakanin palasdinawa masu Zanga-zanga da sojojin Sahayoniya, ya yi sanadin shahadar bapalasdine guda da jikkatar wasu da dama.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, Cibiyar  labarai ta Palasdinawa ta ambaci cewa dukkan palasdinawa ne suka fito kan titunan yammacin kogin jordan da yankin Gaza domin nuna kin amincewarsu da matsayar shugaban kasar Amurka na daukar Kudus babban birnin haramtacciyar Kasar Isra'ila.

A garin al-Khalil da ke yammacin kogin Jordan, sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila da ke kan dawakai  da kasa, sun yi amfani da albarusai akan masu Zanga-zangar tare kuma da harba hayaki mai sa hawaye.

A birbin kudus ma masu Zanga-zangar sun rika bada taken tir da matakin na Amurka tare da jaddada cewa birnin Kudus na larabawa da musulmi ne.

Sauran garuruwan yankin yammacin kogin Jordan da aka yi Zanga-zangar sun kunshi Jenin, Nablus, Tul Karam da Ramallah.

A kasashe da dama na duniya ma an gudanar da Zanga-zangar yin tir da Amukra da matakin da shugabanta ya dauka akan masallacin Kudus.

3670519

 

 

 

 

captcha