IQNA

Taron Makon Hadin Kai A Kasar Senegal

20:17 - December 09, 2017
Lambar Labari: 3482184
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron makon hadin kai karo na biyu a kasar Senegal domin tunawa da hahuwar manzon Allah.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai a bangaren hulda da jama'a na cibiyar al'adun muslunci ya habarta cewa,a  jiya an gudanar da taron makon hadin kai karo na biyu a kasar Senegal domin tunawa da hahuwar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan taro wanda aka gudanar ya samu halartar malamai da kuma masana, wadanda suka gudanar da bayanai a kan matsayin manzon Allah.

Taron makon hadin kai an samar da shi ne tun kimanin shekaru talatin da daya da suka gabata marigayi jagoran juyin juya halin mslunci ne ya ayyana makon haihuwar manzo a matsayin makin hadin kan musulmi.

A wannan taro mabiya darikokin sufaye sun samu halarta, kasantuwar Senegal na daga cikin kasashen Afirka masu yawan mabiya darikun sufaye.

3670686

 

 

 

 

 

 

 

captcha