IQNA

Gwamnatin Uganda Za Ta Shiga Cikin Tsarin Bankin Musulunci

21:08 - February 05, 2018
Lambar Labari: 3482368
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Uganda ta sanar da cewa, za ta shiga cikin tsarin nan na bankin musulunci wada baya ta’ammli da riba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na standardmedia cewa, gwamnatin kasar Uganda ta bayyana shirinta na shiga cikin tsarin nan na bankin musulunci wada baya ta’ammli da riba a dukkanin harkokin kudade.

Wannan mataki na zuwa ne bayan da majalisar dokokin kasar ta duba wannan batu, inda masana tattalin arziki na kasar suka bayar da shawar cewa yin amfani da irin wannan tsari na musulunci zai taimaka ma tattalin azikin kasar.

Yanzu haka dai majalisar dokokin kasa na yin nazarin kan batun, inda daga bisani za a kada kuri’ar amincewa da batun kafin a fara aiwatar da shi.

Kasashe irin su Kenya, Uganda da kuma Ethiopia, suna ganin cewa yin aiki da tsarin tattalin arziki na bankin musulunci zai taimaka wajen raya ayyukan karkara da bunkasa tattalin arzikinsu.

Wasu daga cikin kasashen Afika da suka hada da Ngeria, Morocco da Senegal tuni suka fara yin aiki da wannan tsari.

Adadin musulmi kasar Uganda ya kai 16 cikin dari daga cikin mutane miliyan 37 da kasar take da su.

3688845

 

 

  

 

captcha