IQNA

Qasemi: Isra’la Tana Son Wawantar Da Duniya Kan Ta’addancinta A Kasashen Musulmi

18:43 - February 10, 2018
Lambar Labari: 3482382
Bangaren kasa da kasa, mai mgana da yawun ma’aikatar harkokin kasar Iran Bahram Qasemi ya mayar da martani dangane da hare-haren da Isra’ila ke kaiwa kan Syria.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da yake mayar da martani a yau kan hare-haren da Isra’ila ke kaiwa kan Syria, Qasemi ya bayyana cewa har kullum Isra’ila tana son ta rika wawantar da al’ummomin duniya kan ta’addancinta a kan kasashen musulmi.

Ya ce Syria tana hakkin ta yi amfani da karfinta domin kare kasarta daga duk wani shishigi da wani zai iya yi mata, kamar yadda dokokin kasa da kasa sun amince da hakan, kuma kakkabo jirgin Isra’ila da ya kai hari a Syria hakan yana bisa ka’ida, bai sabawa ko daya daga cikin dokokin majalisar dinkin duniya.

Dangane da babatun da Isra’ila da wasu daga cikin kasashen da ke mara mata baya a yankin suke na cewa Iran tana shiga cikin harkokin Syria, Qasemi y ace Iran ta shiga a Syria ne  bisa gayyatar halastacciyar gwamnatin Syria, kuma Iran tana baiwa gwamnatin Syria shawarwari kan dubarun yaki domin kare kasarta, wannan kuma ana yi a ko’ina cikin duniya.

3690402

 

 

captcha