IQNA

Taro Na Farko Kan Bankin Musulunci A Ghana

23:18 - February 14, 2018
Lambar Labari: 3482396
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da zaman taron kara wa juna kan harkokin bankin musulunci a kasar Ghana.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin watanni biyu masu zuwa za a gudanar da zaman taron kara wa juna kan harkokin bankin musulunci a kasar Ghana a ranakun 25 da 26 ga watan Afirilun 2018, tare da halartar wakilai daga kasashen Malaysia, Singapore, Pakistan, Najeriya da kuma Iran.

Tsohon gwamnan babban bankin kasar Ghana shi ne zai jagoranci zaman taron, wanda zai gudana a cikin babban dakin taruka na jami’ar Ghana.

Haka nan kuma za a gabatar da makaloli kan batun bankin muslunci da kuma harkokin ajiyar kudi a musulunce, inda za a zabi makala mafi kyau domin yadawa.

3691512

 

 

captcha