IQNA

Paraguay Ta Bude Ofishin Jakadancinta A Quds

23:03 - May 21, 2018
Lambar Labari: 3482679
Bangaren kasa da kasa, kasar Paraguay ta bude ofishin jakadancinta a hukumance a birnin Quds mai alfarma domin yin koyi da gwamnatin Amurka.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya kasar Paraguay ta bude ofishin jakadancinta a hukumance a birnin Quds mai alfarma domin amincewa da wannan birni a matsayin babbar birnin haramtacciyar gwamnatin yahudawan Ira’ila.

Jaridar Albayan ta kasar hadaddiyar daular larabawa ta rubuta cewa, tun bayan da Amurka ta bude ofishin jakadancnta a makon da ya gabata, lamarin yake ci gaba da fskantar tofin Allah sine a duniya, da kuma tsakanin al’umma Palastinu, wadanda Isra’ila ta kasha kimanin mutane 65 daga cikin a kasa watanni biyu, wadanda suke nuna rashin amincwa da mama kasarsu.

A ranar Laraba da ta gabata ma kasar Guatimala ta mayar da nata ofishin jakadancin zuwa Quds, tare da halartar shugaban kasar Jimmy Morales.

3716435

 

 

 

 

 

 

 

captcha