Kamfanin dillacin labaran iqna ya habarta cewa, shafin jarida Al-ahram ta kasar Masar ya bayar da rahoton cewa,a lokacin da Muhammad Salah yake amsa tambaya kan cewa ko za yi azumi a ranar wasan karshe na cin kofin nahiyar turai, ya amsa da cewa warai kuwa.
Ya ce tun da aka fara azumi a kowace rana yana yin azumi, kuma a ranar da za a buga wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar turai a karshen wannan mako zai yi azumi kamar yadda ya saba.
Muhammad salah dai shi ne ya lashe kyautar dan wasan da ya fi zura kwalle a wasan kasar Ingila na wannan bazarar wasanni, inda ya saka kwallaye 32.
A ranar Asabar mai zuwa za a buga wasan karshe tsakanin Liverpool da Real Madrid a birnin Kiev na kasar Ukraine.