IQNA

Masarautar Bahrain Ta Kwace Hakkin Zama ‘Yan Kasa Daga Mutane 732

23:48 - May 23, 2018
Lambar Labari: 3482688
Bangaren kasa da kasa, wani rahoton da wata kungiyar kare hakkin bil adama ta fitar ya nuna cewa, masarautar Bahrain ta kwace hakkin zama dan kasa daga mutane 732 saboda dalilai na siyasa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta Lu’ulu’a ta bayar da rahoton cewa, a jiya wata kungiyar kare hakkin bil adama ta fitar da rahoton da ya tabbatar da cewa, masarautar Bahrain ta kwace hakkin zama dan kasa daga mutane 732 saboda dalilai na siyasa da bangaranci na aida.

Kungiyar ta ce daga cikin mutanen da aka janye wa hakkinsu na zama yan kasa har da wasu daga cikin manyan malamai, ‘yan siyasa, mambobin majaisar dokoki, da kuma masu rajin kare hakkokin bil adama gami da ‘yan jarida.

Rahoton kungiyar ya kara da cewa, a ranar 7 ga watan Nuwamban 2012 ne aka fara zartar da hukuncin kwacewa yan asalin kasar hakkinsu na zama ‘yan kasa, saboda dalilai na siyasa da kama karya, daga ciki kuwa har da manyan malamai na kasar uku wato Ayatollah Isa Kasim, Ayatollah Husain Najati, da Ayatollah Muhammad sanad.

3716981

 

 

 

 

 

captcha