IQNA

An Tarjama Kur’ani A Cikin Harshen Luhya A Kenya

23:26 - July 31, 2018
Lambar Labari: 3482846
Bangaren kasa da kasa, an tarjama kur’ani mai tsarki a cikin harsen Luhya daya daga cikin fitattun harsuna a kasar Kenya.

 

Kamfain dillancin labaran iqna ya habarta cewa, yanz haka an kammala aikin tarjamar kur’ani mai tsarki a cikin harsen Luhya daya daga cikin fitattun harsuna a kasar Kenya wanda wasu gungun malamai suka yi.

Wata cibiya da ake kira cibiyar sirar manzon Allah (SAW) ce ta dauki nauyin aikin tarjamar.

Yanzu haka dai ana ci gaba da kara duba wannan tarjama kafin daga karshe a kai ga matasaya ta bai daya kain gyaran dak aka yi.

Ana sa ran dai kafin karshen wannan shekara da muke ciki ne za a buga wannan kur’ani da aka tarjama a cikin harshen Luhya a karon farko.

3734617

 

 

 

captcha