IQNA

Horo Ga Masu Kula Da Ayyukan Masallata A Lokutan Aikin Haji A Madina

23:57 - August 02, 2018
Lambar Labari: 3482855
Bangaren kasa da kasa an gudanar da wani kwarya-kwaryan shiri na bayar da horo kan yadda ake yin mu’amala da alhazai a masallacin annabi.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a daidai lokacin da ake shirin fara ayyukan hajjin bana, an gudanar da wani shiri na bayar da horo kan yadda ake yin mu’amala da alhazai a masallacin annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa a birnin Madina ma alfarma.

Babbar manufar shirin da ita ce koyar da ma’aikata a masallatai sanin yadda za su yi mu’amala da baki da suka fito daga kasashen duniya domin sauke farali.

Sulaiman Abdullah bin Abdullah Rumi ya bayyana cewa, aiwatar da wannans hiri yana da matukar amfani, domin hakan zai kara kare mutuncin kasar da ke daukar bakuncin taron na hajji.

3735421

 

 

 

 

 

captcha