IQNA

Za A Gudanar Da Aikin Gyaran Masalacin Jinin A Masar

23:46 - October 18, 2018
Lambar Labari: 3483052
Bangaren kasa da kasa, za a gudana da aikin gyaran masallacin tarihi na  Jinin na kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an fara gudanar da aikin gyaran masallacin tarihi na Jinin a  kasar Masar da ke garin na Jinin.

An fara gudanar da aikin ne tare da halartar masana kan harkokin gini daga ciki da wajen kasar ta Masar, musamman ma daga wasu daga cikin kasashen larabawa.

Wannan masallaci dai yana daga cikin masallatai da aka saka su a matsayin masallatai na tarihi a kasar ta Masar.

An gina masallacin Jinin a cikin karni na biyar hijira kamariyya, kuma har yanzu ana daukarsa a matsayin wuri na tarihi a kasar.

3757025

 

 

 

 

 

captcha