Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin samar da ruwan sha na kwalba na Naba a birnin Najaf na Iraki ya samar da robobin ruwan sha guda miliyan 10 domin masu ziyarar arbaeen na Imam Hussain.
Bayanin ya ce kamfanin ya rika samar da rubobi dubu 300 ne a kowace rana tun daga makonnin da suka gabata, inda ya zuwa yanz ya tanadi robobi miliyan 10 na ruwan sha da zai raba su kyauta ga masu ziyarar Imam Hussain (AS).