IQNA

'Yar Majalisar Dokokin Amurka Musulma Ta Mayar Wa Trump Da Martani

22:55 - February 15, 2019
1
Lambar Labari: 3483374
'Yar majalisar dokokin kasar Amurka musulma Ilhan Umar ta mayar wa shugaban Amurka Donald Trump da martani, bayan da ya bukaci ta yi murabus daga aikin 'yar majalisa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Arabi Post ya bayar da rahoton cewa, Donald Trump ya zargi Ihan Umar da nuna kiyayya ga yahudawa, a kan haka ya bukaci ta yi murabus daga aikinta na 'yar majalisar dokokin kasar Amurka.

A lokacin da take mayar masa da Martani, Ilhan ta bayyana cewa, tun daga lokacin da Trump ya hau shugabancin kasar Amurka yake nuna gaba da musulmi da bakin da suka yi hijira zuwa kasar da bakaken fata har ma ga yahudawa da kiristocin da suke adawa da salon siyasarsa, ta ce dauki darasi daga furucin da aka yi kan kalamanta, amma shi wane darasi ya dauka?

A ranar Lahadin da ta gabata ce Ilhan ta yi wani rubutu a shafinta na twitter, inda ta caccaki gwamnatin Amurka kan yadda take kare manufofin Isra'ila da kuma goyon bayanta ido rufe, lamarin da ya jawo fushin wasu daga cikin mahukuntan kasar ta Amurka da ma wasu kungiyoyin yahudawa masu goyon bayan Israila.

Daga bisani Ilhan ta bayyana cewa ita bata adawa da yahudawa, tana adawa ne da salon siyasar zalunci, amma wadanda suka fusata a kan kalamanta su yi hakuri, amma duk da haka Trump ya kiraye ta da ta yi murabus, kiran da ta yi watsi da shi.

A nata bangaren Katty Halber wata bayahudiyya mai fafutuka  akasar Amurka tana goyon bayanta ga Ilhan Umar, inda ta ce sukar Isra'ila ba yana nufin sukar yahudawa ko addinin yahudanci ba ne, Isra'ila daban yahudawa da addinin yahudanci daban, a kan haka abin da Ihan ta fada gaskiya ne, domin yahudawa da dama a duniya basa goyon bayan Ira'ila

3790054

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Hussaini umar dankanti
0
0
Allah yataimakeki ilham wajen kwato yan cin musulmai da ake ciwazarafi a amurka
captcha