IQNA

Gwamnatin Palastie Ta Samu Taimakon Dala Biliyan 36 Daga Lokacin Da Aka Kafa Ta

22:59 - February 15, 2019
Lambar Labari: 3483375
Kwamitin tattalin arziki na gwamnatin Palastine ya ce daga lokacin kafa gwamnatin ya zuwa yanzu sun karbi taimakon kudade na kimanin dala biliyan 36 daga kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Kwamitin kula da tsare-tsaren harkokin tattalin arziki na gwamnatin kwarya-kwaryan cin gishin kai ta Palastine ya ce daga lokacin kafa gwamnatin ya zuwa yanzu ya karbi taimakon kudade na kimanin dala biliyan 36.

Rahoton da kwamitin ya fitar a jiya ya tabbatar da cewa, daga lokacin kafa gwamnatin kwarya-kwaryar cin gishin kai ta Falastinawa an bayar da taimakon kudade da suka kai dala biliyan 36.5, sai kuma bashi wanda ya kai dala biliyan 106 daga kasashen duniya.

Bayanin ya ce an karbi wannan taimakon kudaden ne daga shekara ta 1994 zuwa 2017.

3790009

 

captcha