IQNA

Wata Kotu Ta Soke Hukuncin Rufe Wasu Masallatai A Austria

23:04 - February 15, 2019
Lambar Labari: 3483376
Wata kotu a kasar Austria ta soke hukuncin rufe wasu masallatan musulmi guda 6 a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, jridar Milliyat ta kasar Turkiya ta bayar da rahoton cewa, kotun birnin Vienna ta yanke hukuncin cewa, umarnin da gwamnatin Austria ta bayar na rufe wasu masallatai 6 a cikin birnin na Vienna ya sabawa doka.

Kotun ta ce bisa ga dalilai da suka hada da rashin bayar da wa'adi cikin lokaci, da kuma rashin kwararn dalilai da za su iya sanya a rusa wurin bauta bisa tsarin dokokin kasar, ta rusa umarnin da gwamnati ta bayar na rusa wadannan masallatai, domin hakan ya yi hannun riga da dokokin da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar.

A 'yan watannin da suka gabata ne gwamnatin kasar Austria ta bayar da umarnina  rufe wasu masallatai a kasar, bisa zargin cewa masu tsatsauran ra'ayi na yin amfani da masallatan wajen tunzura musulmi domin shiga ayyukan ta'addanci.

A cikin 'yan shekarun baya-bayan nan dai kyamar musulmi ta karu matuka a tsakanin al'ummar kasar Austria, sakamakon ayyukan ta'addanci da wasu suke aikatawa a cikin kasashen turan da sunan jihadi, wanda hakan ya bayar da dama ga kungiyoyi masu adawa da musulunci a cikin kasashen turai suka samu damar da za su bata addinin muslucni da cin zarafin musulmi.

3790240

 

captcha