IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Kur’ani Ta share Fage A Mauritania

23:46 - February 19, 2019
Lambar Labari: 3483385
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta share fage a yau a kasar Mauritaniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a an fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta share fage a yau a kasar Mauritaniya a birnin Nuwakshout fadar mulkin kasar.

Ahmad Wuld Ahlu Dawud ministan kula da harkokin kula da addinin a kasar Mauritaniya da ya halarci wurin bude taron gasar ya bayyana cewa, wannan lamari mai matukar muhimmanci.

Ya ce a halin yanzu lamarin kur’ani shi ne kan gaba wajen daidaita tunanin matasa, wanda ya kamata dukkanin bangarori na malamai da iyaye da mahukunta ya kamata su mayar da hankalia  kansa.

Matasa kimanin 300 ne daga sasas na kasar ta Mauritania suke halartar wannan gasa, wadanda suka hada da mardata da kuma makaranta.

3791354

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha