IQNA

Jam’iyyar Republican Ta Nisanta Kanta Da Cin Zarafin Ilhan Umar

23:56 - March 04, 2019
Lambar Labari: 3483423
Jam’iyyar Republican a reshenta da ke jahar Virginia  a kasar Amurka ta nisanta kanta da cin zarafin da aka yi wa ‘yar majalisar dokokin kasar musulma.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Shafin yada labarai na NPR ya bayar da rahoton cewa, a jiya Jam’iyyar Republican a reshenta da ke jahar Virginia a kasar Amurka ta nisanta kanta da cin zarafin da aka yi wa Ilhan Umar ‘yar majalisar dokokin kasar ta Amurka saboda tana musulma.

Wannan kuwa ya zo ne bayan taron da jam’iyyar ta yi a ranar Asabar da ta gabata, inda wasu ‘yan jam’iyyar suka lika wani babban hoto na harin 11 ga watan Satumban 2001, kuma suka rubuta cewa “kun ce ba za ku taba mantawa ba, amma kun manta”  bayan wannan jumlar sai aka saka hoton Ilhan Umar tana sanye da lullubi na musulunci.

Shugaban jam’iyyar Republican a jahar Virginia Melody Potter ya bayyana cewa, wadanda suka yi wannan ba da sunan jam’iyyarsu suka yi hakan ba, kuma su ba su goyon bayan hakan.

A nata bangaren Ilhan Umar ta mayar da martani a shafinta na twitter da cewa, wannan bai bata mamaki ba, domin kuwa hatta a unguwar da take an yi rubutu a wani babban allo a gefen wani gidan mai, ana yin kira da a kashe Ilhan Umar.

3794778

 

captcha