IQNA

Iran Ta Dakatar Da Aiki Da Wani Bangaren Yarjejeniyar Nukiliya / Ta Bada Wa'adin Kwanaki 60

23:54 - May 08, 2019
Lambar Labari: 3483618
Kasar Iran ta sanar a yin watsi da yin aiki da wani bangaren yarjejeniyar nukiliya wanda ta cimmwa tare da kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna , sakamakin kin aiki da yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da Iran da kuma yin fatali da ita daga bangaren Amurka, da kuma kakaba takunkumai kan Iran, bisa bangarori na 26 da 36 Iran ta dakatar da aiki da wani bangaren yarjejeniyar. Shugaban hukumar makamashin nukliya ta kasar Iran ya bayyana cewa daga yau Laraba takwas ga watan Mayu gwamnatin kasar Iran ta yi watsi da iyakan da aka kayyade mata a yerjejeniyar shirin nukliyar kasar wacce ta cimma da manya-manyan kasashen duniya a shekara ta dubu biyu da sha biyar.

Ya kara da cewa daga yau Iran zata ci gaba da sarrafa makamashin yuranium, fiye da koligram dari uku, sannan zata gasa makamashin na yuranium  da kuma samar da ruwan makamashin nukliyan mai nauyi fiye da ton dari da talatin. Y a kara da cewa, a cikin maadda ta ashirin da shida na yerjejenyar Nukliyar da kasar cimma da manya-manyan kasashen duniya, an bawa kasar Iran damar yin watsi da wani bangaren na yerjejeniyar a duk lokacinda ta ga cewa wani bangare ko wasu bangarorin na yerjejeniyar sun kasa cika nasu alkawulaa yerjejeniyar, don ta jawo hankalinsu kan lamarin.

Daga karshe ya kara da cewa, a halin yanzu Iran zata ci gaba da sayar da ruwan makamashin nukliya mai nauyi wanda ta dakatar saboda yerjejeniyar, sannan, nan da kwanaki sattin za ta ga abinda sauran kasashen da suka amince da yerjejeniyar zasu yi, daga nan zata dauki matakan da suka dace.

 

3809847

 

captcha