IQNA

Qatar Ta Bukaci Saudiyya Da Ta Fitar Da Siyasa A Cikin Batun Aikin Hajji

23:49 - May 15, 2019
Lambar Labari: 3483641
Gwamnmatin kasar Qatar ta bukaci gwamnatin Saudiyya da ta fitar da duk wani batu na siyasa a cikin batun da ya shafi aikin hajji.

Shafin yada labarai na Qantara ya habarta cewa,acikin sakon da hukumomin kasar ta Qatar suka aikewa mahukuntan Saudiyya, sun bukaci kasar da ta kawo karshen matakan da take dauka da suke kawo tarnaki ga maniyyata na kasar ta Qatar.

Tun a cikin shekara ta 2016 ce dai gwamnatin Saudiyya ta dauki matakin hana jiragen kasar Qatar sauka cikin kasarta saboda takun saka na siyasa da ke tsakaninsu, wanda kuma hakan ya shafi batun aikin hajji, inda dubban maniyyata ba za su iya zuwa kasar ta Saudiyya domin sauke farali ba.

Qatar ta bayyana batun aikin hajji da cewa aiki ne na ibada da Allah ya farlanata a kan bayinsa, yin mfani das hi a matsayin makami na siyasa domin cutar da wasu kasashe da kuma hana musulmin wadannan kasashe sauke wannan farali, ya yi hannun riga da dukkanin ka’idoji na addinin muslunci kamar yadda ya yi sabawa dokoki na kasa da kasa.

3811280

 

captcha