IQNA

Rauhani: Ayatollah Sistani Ne Jigon Hadin Kan Al’ummar Iraki

23:14 - September 30, 2020
Lambar Labari: 3485231
Tehran (IQNA)Shugaban Iran ya bayyana babban malamin addini na Iraki Ayatollah Sistani a matsayin jigo na zaman lafiya a kasar.

Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne a yammacin jiya a lokacin da yake ganawa da sabon jakadan kasar Iraki a kasar Iran, Nasir Abdulmuhsin Abdullah, wanda ya mika wa shugaba Rauhani takardunsa na kama aiki.

Rauhani ya ce Iran da Iraki kasashe ne biyu masu tsohon tarihi da yake komawa zuwa ga dubban shekaru da suka gabata, inda kuma har yanzu wadannan al’ummomi suna tare da juna, duk kuwa da hankoron makiyansu na neman raba su a lokuta daban-daban da suka gabata.

Ya ce babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Sistani shi ne bababn jigo na hadin kan kasa a Iraki, wanda ya hada dukkanin al’ummomin kasar wuri guda, wanda hakan babban abin alfahari ne.

Shi ma a nasa bangaren sabon jakadan Iraki a Iran Nasir Abdullah ya bayyana alaka tsakanin kasashen biyu da cewa ta samu ci gaba a halin yanzu fiye da kowane lokaci a baya, kuma za su ci gaba da yin aiki tare a dukkanin bangarori domin ci gaban al’ummominsu.

 

3926251

 

captcha