IQNA

Mutane 30 ne suka mutu, 56 kuma suka jikkata sakamakon fashewar bam a wani masallaci a Pakistan

16:49 - March 04, 2022
Lambar Labari: 3487011
Tehran (IQNA) Jami’an ‘yan sandan Pakistan sun sanar da cewa, wani abu mai karfi da ya fashe a wani masallaci a birnin Peshawar da ke arewa maso yammacin kasar ya yi sanadin mutuwar mutane 30 tare da jikkata wasu da dama.

Shugaban 'yan sandan Peshawar na Pakistan, Mohammad Ijaz Khan, ya ce fashewar ta afku a lokacin sallar Juma'a a wani masallaci da ke Peshawar, ya kashe mutane 30 tare da jikkata 65 kawo yanzu.
A cewar majiyoyin kasar Pakistan, wani bam mai karfi ya tashi a wani masallacin 'yan Shi'a da ke birnin Peshawar na arewa maso yammacin Pakistan a lokacin sallar Juma'a.
Ya zuwa yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutane 30 sakamakon fashewar bam din, sannan kuma an jikkata dimbin mutanen da suka halarci masallacin, da dama daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.
‘Yan sanda sun ce bam din ya tashi ne a daidai lokacin da ake gudanar da ibada a masallacin Kocha Risaldar da ke tsohon yankin Peshawar.
'Yan sandan Pakistan sun ayyana dokar ta baci a dukkan asibitocin Khyber Pakhtunkhwa bayan tashin bom.
 
https://iqna.ir/fa/news/4040183
 
 

Abubuwan Da Ya Shafa: pakistan Peshawar
captcha