IQNA

Yahudawan Sahyoniya Sun rushe masallaci mai shekaru 800

15:51 - April 13, 2024
Lambar Labari: 3490977
IQNA - A ci gaba da lalata wuraren tarihi a zirin Gaza, gwamnatin sahyoniyawan ta lalata wani masallaci mai cike da tarihi na "Sheikh Zakariyya" da ya shafe shekaru 800 yana a gabashin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, a ranar Juma’a 24 ga watan Afrilu, jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun lalata masallacin Sheikh Zakariyya mai dimbin tarihi da ke yankin Al-Darj ta hanyar kai hare-hare a gabashin Gaza.

Harin bam din da aka kai a wannan yanki ya yi sanadiyyar rugujewar masallacin da gidajen da ke kewaye da shi. An aiwatar da wannan mataki ne a cikin tsarin manufofin gwamnatin sahyoniyawan na rusa wuraren tarihi a yakin Gaza.

Babban Masallacin Sheikh Zakaria na daya daga cikin tsofaffin masallatan yankin al-Darj da ke birnin Gaza.

Babu wani bayani dangane da ranar da aka kafu, amma a wannan masallaci an binne wani mai suna Sheikh "Zakariya al-Tammari" daga cikin muftin kasar Sham, wanda ya rasu a watan Safar shekara ta 749 bayan hijira, a wannan masallaci, kuma daga baya wannan masallaci sunansa Sheikh Zakariyya. Wannan fitowar ta nuna cewa an gina masallacin da aka ambata a farkon rabin karni na 8.

 

 

4210101

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: fitowa masallaci ambata tarihi mataki gaza
captcha