IQNA

Burtaniya Ba Za Ta Amince Shirin Isra’ila Na Mamaye Yammacin Kogin Jordan Ba

22:52 - July 01, 2020
Lambar Labari: 3484941
Tehran (IQNA) Firayi ministan kasar Burtaniya Boris Johnson ya bayyana cewa, kasarsa ba za ta amince da shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan ba.

Firayi ministan kasar Burtaniya Boris Johnson ya bayyana cewa, kasarsa ba za ta amince da shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan ba.

A wata zantawarsa da jaridar Isra’ila ta Yedioth Ahronoth da ake bugawa a birnin Tel Aviv, Firayi ministan Burtaniya Boris Johnson ya bayyana cewa, yana fatan gwamnatin Isra’ila za ta manta da batun mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan, domin Burtaiya za ta yi aiki ne kawai da iyakokin 1967 da majalisar dinkin duniya ta shata.

Johnson ya ce wanann kudiri na Isra’ila ya saba wa dokoki na kasa da kasa, kuma zai zama tamkar wata kyauta ce ga wadanda suke son tunawa duniya tsohon tarihin Isra’ila, wanda hakan ba abu ne mai kyau ga gwamnatin Isra’ila ba.

A kan haka Boris Johnson ya ce yana yin kira da kuma fatan ganin cewa ba a aiwatar da wanann shiri ba, idan kuma har aka aiwatar da shi, to Burtaniya ba za ta yi aiki da shi ba, domin kuwa ba ta san da zamansa a hukumance ba bisa doka ta kasa da kasa.

Kafin wannan lokacin da firai ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar da sanar da cewa, a yau 1 ga watan Yuli na wanna shekara ta 2020 ce zai fara aiwatar da shirin mamaye yankunan Falastinawa, tare da hade su da sauran yankunan da Isra’ila ta mamaye.

Sakamakon matsin lamabr da Netanyahu yake fuskanta daga kasashen duniya da suka hada har da manyan kawayen Isra’ila masu mara mata baya, hakan yasa shirin nasa ya fuskanci matsala.

3908141

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Burtaniya Boris Johnson
captcha