IQNA

Karimiyan: Rufe Shafukan Kafofin Yada Labarai Na Iran Da Amurka Ta Yi Ya Saba Wa Ka'ida

17:26 - June 30, 2021
Lambar Labari: 3486063
Tehran (IQNA) Kungiyar hadin kan tashoshin rediyo da talabijin na kasashen musulmi ta mayar da kakkausan martani kan rufe wasu shafukan yanar gizo na Iran da Amurka ta yi.

Wannan na zuwa ne a zaman da kungiyar ta gudanar yau a birnin Tehran tare da halartar wasu daga cikin ammbobin kungiyar daga kasashe daban-daban, yayin da kuma wasu suka halarta ta hanayar hotunan bidiyo na yanar gizo, babban sakataren kungiyar Muhammad Ali Karimiyan ya bayyana cewa, wannan mataki na Amurka yana a matsayin take hakkin fadar albarkacin baki.

Ya ce gwamnatin Amurka da sauran kasashen turai sun fi kowa babatu wajen ikirarin kare hakkokin jama’a na fadar albarkacin bakinsu, amma kuma abin da suke yi a kan wasu ya yi hannun riga da hakan, musamman idan lamarin ya shafi kasashe ko wasu bangarori ko kungiyoyi masu ‘yancin siyasa da neman ganin an yi adalci a cikin lamaurran siyasar duniya.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, irin gudunmawar da kafofin yada labarai na kasar Iran da kuam na sauran bangarori masu ‘yancin siyasa suka bayar, wajen bayyana wa duniya zaluncin Isra’ila kan al’ummar falastinu, shi ne babban dalilin daukar wannan mataki.

Kungiyar hadin kan tashoshin rediyo da talabijin an kasashen musulmi tana mambobi daga kasashen duniya daban-daban, wadanda suka hadu kan cewa ba su amince da wannan mataki da gwamnatin Amurka ta dauka ba, na rufe wasu shafukan tashoshin talabijin na kasar Iran, da kuam wasu na yankin gabas ta tsakiya da ake adawa da salon siyasar danniya da mulkin mallaka na manyan kasashen duniya.

captcha