IQNA

An Amince Da Dokar Da Ake Ganin Ta Kin Jinin Muslunci Ce A Faransa

17:19 - July 24, 2021
Lambar Labari: 3486133
Tehran (IQNA) majalisar dokokin Faransa ta aince ad wata doka da ake ganin ta ginu ne akn kin jinin addinin muslunci.

Kafofin yada labaran kasar faransa sun bayar da rahotannin cewa, Majalisar dokokin kasar ta amince da wani kudirin doka mai cike da cece-kuce duk da kakkausar suka daga bangaren ‘yan majalisun jam’iyyun adawa.

Gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ta yi ikirarin cewa ana bukatar dokar ne domin karfafa tsarin gudanar da addini a Faransa, to sai dai masu suka na cewa matakin keta ‘yancin addini ne.

Bayan muhawara ta tsawon watanni bakwai  da akayi ta kai ruwa rana tsakanin bangarorin siyasar kasar, daga karshe ‘yan majalisa su arba’in da tara suka amince da dokar yayin da sha tara suka ki amincewa, sai kuma wasu biyar sukayi rowan kuri’unsu.

 

3985893

 

 

captcha