Shafin yada labarai na Aljuhainah ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da tarukan ranar Idin Ghadir a garin Qatif da ke gabashin kasar Saudiyya.
Wannan taro dai yana daga cikin muhimman taruka da mabiya mazhabar Ahlul bait (AS) suke gudanarwa a ko'ina a cikin fadin duniya, domin tunawa da ranar jawabin karshe da manzon Allah (SAW) ya yi bayan kammala aikin hajjin bankwana.
A bisa ruwayoyi da sahabbai 115 suka ruwaito wanda hakan yasa ruwayar ta zama a matsayin tawatur saboda ingancinta,a ranar ne Manzon Allah (SAW) ya bayyana dan uwansa kuma surukinsa kuma sahabinsa Imam Ali (AS) a matsayin majibincin lamarin muminai a bayansa.
Mabiya mazhabar Ahlul bait a kasar Saudiyya wadanda su ne kashi 15 na al'ummar kasar suna gudanar da irin wadannan taruka na tunawa da wannan rana a yankunansu da suke gabashin kasar.