Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na iqna cewa, wannan tarin kasidu yana nuni da matsayin tafsirin kur’ani da ilimomi a jami’ar Aljeriya tun daga karni na biyu bayan hijira zuwa yau, kuma ya bayyana halin da wannan kasa take ciki a idon mai karatu.
A karshen littafin a bangaren rataye akwai rahoto kan matsayin ilmummukan kur'ani a kasar Aljeriya da kuma rahoton IQNA na yanar gizo da wannan hukuma tare da hadin gwiwar IQNA suka shirya.
A cewar kungiyar al'adun muslunci da sadarwa, an hada tarin kasidun gasar kur'ani mai taken "Algeria da Al-Qur'ani" a matsayin littafi a cikin shafuka 328.
Sai in ce; An gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta "Algeria da kur'ani" a kasar Aljeriya a daidai lokacin da ake gudanar da azumin watan Ramadan tare da halartar farfesoshi da ma'abota tunani na kasar Algeria mai ba da shawara kan al'adun kasarmu.