IQNA

Miliyoyi mutane suna ci gaba da isa kasar Iraki domin halartar tarukan ziyarar arbaeen

16:10 - September 13, 2022
Lambar Labari: 3487848
Tehran (IQNA) miliyoyin masu ziyara daga ciki da wajen kasar Iraki ne suke ci gaba da isa biranan Najaf da Karbala, domin halartar tarukan na Arbaeen.

Yanzu haka dai miliyoyin masu ziyara daga ciki da wajen kasar Iraki ne suke ci gaba da isa biranan Najaf da Karbala, domin halartar tarukan na Arbaeen na Imam Hussain (AS).

Ofishin gwamnan lardin Karbala ya bayar da sanarwar cewa, ya zuwa yanzu miliyoyin mutane suka iso birnin domin halartar wadannan taruka, kuma an dauki dukkanin matakan da suka dace na daukar bakuncin masu ziyara, da hakan ya hada da daukar kwararan matakan tsaro, samar da ababe bukatar rayuwa, da kuma tanadin kayayyakin ayyuka a bangaren lafiya.

Bayanin ya ci gaba da cewa, ya zuwa yanzu fiye da baki miliyan uku ne suka iso Karbala daga kasshe daban-daban, yayin da kuma adadin ‘yan kasar Iraki yah aura miliyan 10.

Ya ce ana sa ran adadin masu ziyarar tarukan Arbaeen a Karbala daga nan zuwa kwanaki biyar masu zuwa, zai kai haura mutane miliyan 20.

A ranar Lahadi mai zuwa ce dai za agudanar da tarukan arbaeen na Imam Hussain (AS) a birnin na Karbala inda hubbarensa yake.

4085144

 

captcha