Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a ranar Laraba da ta gabata wasu gungun kwamandoji da mayaka na tsaron kasa sun gana da jagoran juyin juya halin Musulunci a Husainiyar Imam Khumaini.
A farkon wannan taro, Pourahmadi, fitaccen makarancin kur’ani kuma daya daga cikin jagororin dakarun da suka yi yaki tsaro na tsawon shekaru takwas, ya karanta ayoyin Kalamullah Majid.