Karatun debe kewa tare da kur'ani Mai Girma na Ramadan na shekarar 1445
IQNA - A ranar Talata 12 watan Maris ne aka gudanar da taron debe kewa da kur’ani mai tsarki na watan Ramadan tare da halartar malamai da mahardata daga ko’ina a fadin kasar Iran tare da halartar jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar a Husainiyyar Imam Khomaini (RA). A cikin shirin za a ji karatun matashin nan mai karatun kur'ani mai girma Mohammad Ali Rasoulian daga cikin suratu Naml aya ta 38 zuwa 40 da aka gabatar a wannan taro na kur'ani.