IQNA

Haniyya ya Bayyana Kula Alaka Da Isra'ila Da Sudan Ta Yi Da Cewa Ba Ra'ayin Mutanen Kasar Ba Ne

23:39 - October 25, 2020
Lambar Labari: 3485305
Tehran (IQNA) Isma’il Haniyya ya bayyana cewa, kulla alaka da mahukuntan Sudan suka yi da yahudawan Isra’ila, ba bisa ra’ayin jama’ar kasar suka yi haka ba.

Shugaban kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas Isma’il Haniyya ya bayyana cewa, kulla alaka da mahukuntan Sudan suka yi da yahudawan Isra’ila, ba bisa ra’ayin jama’ar kasar suka yi haka ba.

Jagoran kungiyar ta Hamas ya bayyana cewa, matsayar al’ummar Sudan a bayyane take kan kin amincewa da duk wani nau’in mamaya a kan kasar musulmi da larabawa, tun da ga lokacin da yahudawa suka mamaye Falastinu, har zuwa lokacin da suka kafa abin da suke kira da Isra’ila, kuma har yanzu matsayar al’ummar Sudan kenan.

Ya ce al’ummar falastinu an jinjinawa mutanen Sudan kan yin watsi da matsayar da sabbin mahukuntan rikon kwarya na kasar suka dauka, na mika kai ga yahudawa, da kuma kulla alaka da su,a daidai lokacin da suke ci gaba da yin kisan kiyashi a kan al’ummar Falastinu, da keta alfarmar wurare masu tsarki na musulmi.

Haniyya ya ci gaba da cewa, matsayar al’ummar Sudan ita ce matsayar al’ummomin larabawa da na musulmi dangane da kulla alaka da wasu daga cikin masu ha’inci suke yi tare da yahudawan Isra’ila, na kin amincewa da hakan, amma amma masu mulki da ke samun goyon bayan Amurka da yahudawa suna yin gaban kansu wajen biya wa iyayen gidansu bukata.

Haka nan kuma Haniyya ya yi tir da Allawadai da ci gaba da batuncin da ake yi wa manzon Allah (SAW) a kasar Faransa da sunan ‘yancin fadar albarkacin baki.

3931134

 

captcha