IQNA

Cibiyar Hubbaren Hussaini Za Ta Gudanar Da Taron Karatun Kur’ani A Birnin Qom

18:46 - October 06, 2015
Lambar Labari: 3382528
Bangaren kasa da kasa, cibiyar hubbaren Hussaini ta shirya gudanar da wani na karatun kur’ani mai tsarki domin girmama alhazan da suka rasu a Mina musamman ma makaranta kur’ani mai tsarki.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na QAF cewa, Darul kur’an na hubbaren Hussaini ya dauki nauyin shirya karatun kur’ani mai tsarki domin kai ladarsa ga mahajjata da suka rasu a Mina musaman ma makarantta 5 na kur’ani.



Bayanin ya ci gaba da cewa wannan karatu yana da matukar muhimmanci ga dukkanin ma’abota kur’ani kr’ani mai tsarki na jamhuriyar muslunci ko kuma na sauran kasashen duniya, domin kuwa daga cikin wadanda ska rasu har da manyan makaranta na kasa da kasa.



Taron karatn ya hada wasu daga cikin makaranta na cikin gida kuma wadanda ska zo daga kasashen ketare, domin kara nuna alhini kan bababn rashin da aka yi, wanda ya zama irinsa mafi girma a cikin shekaru ashirin da biyar da suka gabata.



Wannan cibiyar dai ta saba shirya taruka da ska fanganci kur’ani mai tsarkia a birnin na Qom, amma wanann karon taron ya shafi wadanda suka rasu ne sakamakon abin da ya faru a aikin hajjin bana mai matukar tayar da hankali.



A daya bangaren na wannan traon karatun kurani kuma, za a gudanar wata addu’a ta musamman ga daya daga cikin masu hidima ga lamarin kur’ani mai tsarki, musamman marigayi Abbas Ka’abi.



 



3382394

Abubuwan Da Ya Shafa: qom
captcha