IQNA

Wani Malami A Masar:

Azhar Ba ta Da Hakkin Hana Buga Ko Sayar Da Kwafin Kur’ani Mai Launi

23:29 - January 28, 2017
Lambar Labari: 3481180
Bangaren kasa da kasa, sheikh Hassan Aljinani daya daga cikin malaman kasar Masar ya bayyana cewa, Azhar ba ta da hakkin hana a buda ko yada kwafin kur’ani mai launi.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Yam Sabi cewa, sheikh Hassan Aljinani daya daga cikin manyan malaman addini a kasar Masar ya bayyana a wani shiri na talabijin Alnaharwan cewa, Azhar ba cibiya ce ta shari’a ba.

Shehin malamin ya bayyana hakan ne bisa hukunci da kuma umarnin da cibiyar ta Azhar ta bayar ne a kan buga da kuma yada kwafin kur’ani mai tsarki mai launi, inda ta ce hakan baya halasta, kuma ta bayar da umarnin a kwace duk wani kur’ani mai launi da aka buga a kasar.

Wannan mataki na Azhar ya zo ne bayan da wasu malamai suka nuna rashin gamsuwarsu da hakan a kasashen Syria, Lebanon, hadaddiyar daular larabawa da kuma kasar ta Masar, inda ita Azhar ta nuna rashin amincewarta tare da yanke hukunci da kuma bayar da umarni a kan hakan.

Malamin y ace Azhar aikinta shi ne ta duba abin da yake daidai ta karfafa mutane a kan yinsa, abin da yake ba daidai ba kuma ta fahimtar da mutane da yi musu nasiha domin su guje shi, amma yanke hukunci da kuma bayar da umarni na hana buga kur’ani ko wani littafi tare da turawa akwace shia duk inda aka gansu s acikin kasar, wannana ikin gwamnati ne.

3567688


captcha