IQNA

An Gudanar Da Taron Tunawa Da Shahid Al Hani A Karbala

23:53 - July 08, 2017
Lambar Labari: 3481681
Bangaren kasa da kasa, an gudana da taron tunawa da shahid Amin Muhammad Al Hani a hubbaren Imam Hussain (AS) da ke birnin Karbala na Iraki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na qaf cewa, an gudanar da taron tunawa da masanin ku’an mai tsarki malam Amin Muhammad Al Hani shugaban cibiyar kur’ani a yankin Awamiyyaha gabashin saudiyya, wanda maukuntan kasar suka kasha shi.

Daga cikin wadanda suka halarci taron na tunawa da shi ha da Sheikh Saleh Ibrahim mamba akwamitin kula da harkokin al’ummar yankin Qatif.

Taron dai ya sau halarrtar malamai da kuma daliban addini gami da masana,inda aka gabatar da jawabai a kan matsayin wannan bawan Allah wanda ya karar da rayuwarsa baki daya wajen hidima ga kur’ani mai sarki, wanda kuma d ga karshe mahukuntan masarautar Al Saud sun kasha shi ba tare da wani dalili ba.

Tun a cikin watan Ramadan mai alfarma da ya gabata ne jami’an tsaron masarautar ‘ya’yan gida saud suka kaddamar da hari a garin Awamiyya suka kashe wannan malami da dukkanin al’ummar yankin ke alfahari da shi.

Sheikh Saleh Ibrahim yay i godiya alokacin da yake gabatarda jawabinsa a gaban taron wanda ya gudana a hubbaren Imam Hussain (AS) agarin karbala mai alfarma.

3616600


captcha