IQNA

Shari’ar Sheikh Ai Salman Yawo Da Hankalin Jama’a Ne

23:45 - December 29, 2017
Lambar Labari: 3482248
Bangaren kasa da kasa, hukumar kare hakkin bil adama da kuma kare dimukradiyya da ke da mazauni a Amurka ta bayyana shari’ar mahukuntan Bahrain kan sheikh Ali Salman da cewa wasa da hankulan jama’a ne.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Hussain Abdullah shugaban hukumar kare hakkin bil adama da kuma kare dimukradiyya da ke da mazauni a Amurka ya bayyana cewa, shari’ar da mahukuntan Bahrain suka ce suna yi kan sheikh Ali Salman ba wa ani abu ba ne illa wasa da hankulan al’ummomin duniya ne.

Ya ce mahukuntan masarautar kama karya ta Bahrain tana son yin amfai da batun gurfanar da shikh Ali Salman domin cimma wasu manufofi na siyasa  adaidai wannan lokaci.

Masarautar kama karya ta Bahrain dai ta kama sheikh Ai salma ne tuna  cikin watan Dsamban 2014 ne, bisa hujar cewa yana da alaka da gwamnatin Qatar, kuma yana shirin kifar da masarautar kasar ta Bahrain.

Cibiyar ta bukaci mahukuntan masarautar kama karya ta Bahrain da su gaggauta sakin sheikh Ali Salman da suke tsare da shi bisa dalilai na siyasa, da kuma neman murkushe duk wani mai yunkurin ganin an samu mulki da shugabanci na adalci da yin daidaito tsakanin ‘yan kasa.

3677307

 

 

 

captcha