IQNA

Kira Zuwa Ga Katse Internet Ga ‘Yan Ta’adda A Masar

22:53 - February 27, 2018
Lambar Labari: 3482437
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Ali Sulaiman masani kan harkokin sadarwa a kasar Masar ya bayyana cewa babban abin da ya kamata a yi domin rage yaduwar akidar ta’addanci shi ne katse layukansu na internet.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na INA cewa, Ahmad Ali Sulaiman masani kan harkokin sadarwa  a kasar Masar ya bayyana cewa babban abin da ya kamata a yi domin rage yaduwar akidar ta’addanci shi ne katse layukansu na internet domin ta wannan hanyar ne suke yada akidunsu cikin sauri a duniya.

Masanin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani bayani a gaban taron karawa juna sani kan harkokin ‘yan ta’adda na kasa da kasa, da ake gudanarwa a Masar.

Bayanin ya ci gaba da cewa, da dama daga cikin masana suna ganin cewa yaduwar akidun ta’addanci cikin sauria  duniya abu ne wanda aka shirya shi, kuma manyan kasashen duniya suna da hannu a cikin lamarin, duk kuwa da cewa asalin akidun ta’addanci sun samo asali ne daga tunanin wasu daga larabawa, amma suna yada su ne tare da taimako da amincewar turawan.

Masu wanann ra’ayi suna ganin cewa, bababr manufar kasashen turawa da suke taimaka ma kasashen larabawa masu yada ta’addanci ita ce bata sunan muslunci a idon duniya, kuma abin yake faruwa Kenan.

3695187

 

 

 

 

 

captcha