A cikin wani bayani da ta rubuta a shafinta na twitter, Ilhan Omar ta bayyana cewa; takunkumin Amurka yana da babban tasiri wajen cikas ga yunurin Iran an murkushe cutar Corona a kasar, a daidai irin wannan lokacin ne kuma gwamnatin Amurka take kara tsananta takunkumin, ta ce wannan shi ne zalunci mafi girma.
Ta ci gaba da cewa, baya ga takunkumi a bangaren kayayyain kiwon lafiya, shi ma takunkumin tattalin arzikin Amurka a kan kasar wani nau’i ne na zalunci.
A ranar Alhamis da ta gabata ce Amurka ta sanar da kara tsananta takunkuminta akan Iran, biyo bayan kiraye-kirayen da bangarori na duniya suka yi wa Amurka, na janye takunkumanta akan kasar ta Iran, domin samun sauki yaki da cutar corona.