IQNA

Yahudawan Ethiopia 316 Sun Isra’ila A Yau

22:30 - December 03, 2020
Lambar Labari: 3485426
Tehran (IQNA) yahudawan Ethiopia 316 sun isa birnin Tel aviv a yau bayan da gwamnatin Isra’ila ta ba su damar yin hijira daga kasarsu.

Kamfanin dillancin labaran Anadulo ya bayar da rahoton cewa, a yau firayi ministan Isra’ila Benjuamin Netayahu, tare da ministan yaki gami da ministan harkokin wajen gwamnatin yahudawa, sun isa filin sauka da tashin jiragen sama na Ben Gurion, domin tarbar yahudawan Ethiopia.

A lokacin tarbarsu, Netanyahu ya bayyana cewa, wannan tana daya daga cikin ranar farin ciki a wurinsu bayan isowar wannan adadi na yhudawa daga Habasha, kuma a gobe juma’a wasu karin 100 za sui so Tel Aviv.

A cikin watan Oktoban da ya gabata ne majalisar ministocin Isra’ila ta amince da daftarin kudiri, wanda ya bayar da damar yin hijira ga yahudawa 2000 daga kasar Habasha zuwa Isra’ila, daga nan zuwa kafin shekara mai kamawa ta 2021.

A ranar Talata da ta gabata ce ministar Isra’ila mai kula da harkokin yahudawa masu yin hijira zuwa Isra’ila ta isa kasar Habasha, wadda ita ‘yar asalin kasar ce, domin kwaso yahudawan da za su yi hijira daga kasar zuwa Isra’ila.

3938904

 

 

captcha