Dubban Falastinawa ne suka yi ba ta kashi da yahudawa a jiya biyo bayan farmakin da jami’an tsron Isra’ila suka kaddamar a kansu a birnin Quds.
Tashar Alalam ta bayar da rahoton cewa, tun da jijjifin safiyar jiya Juma’a ne Isra’ila ta baza jami’an tsaro masu yawa a cikin birnin Quds, da nufin hana musulmi gudanar da sallar Juma’a a cikin masallacin Aqsa mai alfarma.
Duk da matakan da Isra’ila ta dauka, fiye da musulmi dubu 60 suka gudanar da sallar Juma’a a ciki da wajen masallacin, yayin da kuma ta hana wasu dubban isa zuwa masallacin.
Wannan dai na zuwa sakamakon tsokanar da yahudawa masu tsatstsauran ra’ayi suke yi wa Falastinawan birnin Quds ne, inda cikin wannan makon yahudawan suke kai hare-hare kan Falastinawa tare da cin zarafinsu, inda kuma yahudawan da suke yin hakan suke samun kariya da tsaro daga jami’an tsaron gwamnatin Isra’ila.
Ko a daren jiya an yi ba ta kashi tsakanin jami’an tsaron gwamnatin yahudawan da kuma matasan falastinawa, inda aka jikkata da dama daga cikin falastinawa tare da kame wasu.