IQNA

Jami'an Tsaron Saudiyya Sun Murkushe Masu Juyayin Shahadar Imam Hussain (AS)

19:36 - August 12, 2021
Lambar Labari: 3486194
Tehran (IQNA) jami'an 'yan sanda na masarautar Saudiyya sun kai farmaki a kan masu tarukan juyayin dararen Muharram a yankin Qatif.

Shaifin jaridar Al-ahad ya bayar da rahoton cewa, jami'an 'yan sanda na masarautar Saudiyya sun kai farmaki a kan masu tarukan juyayin dararen Muharram na Ashura a yankin Qatif da ke gabashin kasar.

A yayin kai farmakin an kame mutane da suka hada har da limaman masallatai da kuma wasu daga cikin malamai masu gabatar da jawabai kan hakikanin abin da ya faru da zuriyar manzon Allah (SAW) a tarihi a cikin irin wadannan ranaku na goman farko na watan Muharram.

An saki wasu daga cikin limaman bayan cin su tara ta kudi da bai gaza riyal dubu 60 ba a kan kowanensu, tare da yin barazana a kansu matukar dai suka sake gudanar da irin wadannnan taruka ko kuma jawabai a kan wadannan ranaku na Muharram.

Wannan dai ba shi ne karon farko da hakan ke faruwa  a kan mutanen yankunan gabashin kasar Saudiyya ba, wadanda akasarinsu mabiya mazhabar ahlul bait (AS) ne da suke raya duk wani lamari da ya shafi manzon Allah (SAW) ko kuma alayen gidansa.

 

captcha