IQNA

Ministan Harkokin Wajen Serbia Ya Bayar Da Kyautar Kur'ani Na Farko Da Aka Tarjama A Cikin Harshen Serbia Ga Azhar

22:24 - August 24, 2021
Lambar Labari: 3486237
Tehran (IQNA) ministan harkokin wajen kasar Serbia ya bayar da kyautar kur'ani tarjamar harshen Serbia na farko a tarihi ga cibiyar ilimi ta Azhar.

Shafin yada labarai Misri Yaum ya bayar da rahoton cewa, a a ziyarar da yake yi a kasar Masar a yau ministan harkokin wajen kasar Serbia Nicolas Solocovich ya bayar da kyautar kur'ani tarjamar harshen Serbia na farko a tarihi ga cibiyar ilimi ta Azhar.

Ministan ya ce wannan kwafin kur'ani yana da matukar muhimmanci ga dukkanin al'ummar kasar Serbia, amma kasantuwar Azhar na babbar cibiyar ilimi ta musulunci,a  madadin al'ummar serbia ya bayar da kyautar wannan kwafin kur'ani ag wannan cibiya.

Kasar Serbia dai tana da kyakkayawar alaka da kasar Masar, musamman ma tun bayan yakin Bosnia da aka yi, inda daga bisani aka yi sulhu kuma sabiyawan suka nuna nadama kan abin da wasu daga cikinsu aikata kan musulmi.

A halin yanzu dai cibiyar azhar ta karbi wannan kwafin kur'ani, tare da sanya shi a cikin jerin littafaii na tarihi da take adanawa.

 

 

 

 

3992735

 

captcha