Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, an bude bangaren harshen Portuguese a matsayin harshe na 21 na kamfanin dillancin labaran kur'ani na kasa da kasa, a daren jiya a wajen baje kolin nuna ayyuka da nasarorin da aka samu a jami'oin Iran, tare da halartar Hojjatoleslam Mustafa Rostami Wakilin Jagora a jami'o'i, da Mohammad Hossein Hassani, shugaban kamfanin dillancin labaran iqna.
Mostafa Rostami ya ziyarci baje kolin nuna ayyuka da kuma kwarewa da nasarorin da jami'oi suka samu, inda ya duba rumfar IQNA da kuma cibiyar kula da harkokin kur'ani ta kasar.
Kaddamar da harsunan IQNA ya samo asali ne daga kwarewar da wannan kafar yada labarai ta samu ne da kuma bayyana bukatun musulmi da yanayin da suke ciki a kasashen duniya da bayar da cikakkun labarai da rahotanni masu amfani ga musulmi a cikin harsuna daban-daban.
jimlar mutane miliyan 270 ke magana da harshen Portuguese ko dai a matsayin harshen kasa na farko, ko kuma harshensu na biyu, musamman wasu daga cikin kasashen da Portugal ta yi wa mulkin mallaka.
Wannan yare Harshen hukuma ne a ƙasashe tara da suka haɗa da Portugal, Brazil, Mozambique, Angola, Guinea-Bissau, Timor-Leste, Equatorial Guinea, Cape Verde, Sao Tome da Principe, Har ila yau ana yaren Portuguese a Macau.