IQNA

Yahudawan Sahyuniya Sun Ci Zarafin Manzon Allah (SAW)

16:42 - May 29, 2022
Lambar Labari: 3487357
Tehran (IQNA) Yahudawan sahyoniya sun yi ta tururuwa daga yammacin Kudus daga titin Jaffa a Hebron zuwa yankin Bab al-Amud.

Rahoton kafofin Falastinawa ya bayyana cewa mazauna yankin sun ce yahudawan sun yi kokarin tada hankalin ‘yan jarida ta hanyar kai musu hare-hare da kalaman batanci da taken “Mutuwa ga Larabawa”.

Ya kara da cewa, gungun yahudawa ‘yan share wuri zauna na kutsa cikin harabar masallacin Quds, duk da cewa matasan Falastinawa sun yi kokarin tare su, amma jami’an tsaron Isra’ila dauke da muggan makamai suna basu kariya.

Kungiyoyin Falastinawa sun yi Allawadai da cin zarafin al’ummar musulmi da masallacin Quds mai alfarma da yahudawa suka yi.

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa wasu daga cikin yahudawan da suka kutsa kai cikin masallacin Quds sun ci zarafin manzon Allah (SAW).

راهپیمایی پرچم و توهین صهیونیست‌ها به حضرت محمد (ص)

4060582

 

Abubuwan Da Ya Shafa: muggan makamai kariya larabawa batanci musulmi
captcha