IQNA

Hazakar wani yaro dan kasar Masar wajen haddar Al-Qur'ani

16:38 - May 02, 2023
Lambar Labari: 3489077
Tehran (IQNA) Sashen Al-Azhar mai kula da harkokin kur’ani mai tsarki ya fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna irin hazakar wani yaro dan shekara 5 dan kasar Masar wajen haddar kur’ani mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sada al-Balad cewa, Sheikh Abulazid Salameh shugaban sashen kula da harkokin kur’ani na Azhar Al-Sharif ya fitar da wani faifan bidiyo na wata baiwa ta wani yaro dan shekara 5 dan kasar Masar.

A cikin wannan faifan bidiyon, Abdullah Muhammad Abd al-Fattah al-Sayed dan shekara 5 ya bayyana wanda ya haddace kur'ani mai tsarki gaba daya.

Sheikh Hassan Abdul Nabi Iraqi mataimakin kwamitin gyaran kur'ani kuma mai kula da gasar kur'ani a kasar Masar, ya yiwa wannan yaro baiwar tambayoyi, inda ya amsa dalla-dalla.

 

4137944

 

captcha