IQNA

Buga tarjamar kur'ani 100,000 cikin harshen Sweden a Kuwait

15:25 - July 11, 2023
Lambar Labari: 3489452
Kuwait (IQNA) Babban kungiyar da'awar kur'ani da sunnar ma'aiki da ilimomin kur'ani da sunnah ta kasar Kuwait ta sanar da buga kwafin kur'ani mai tsarki 100,000 cikin harshen Sweden a wannan kasa.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Rai cewa, Fahad Al-Dihani shugaban hukumar kula da harkokin yada alkur’ani da sunnar ma’aiki ta kasar Kuwait ya bayyana cewa: Wannan kungiya ta yi daidai da aikin da majalisar ministocin kasar Kuwait ta dora mata. Bayanin shugaban wannan majalisa na buga kwafi 100,000. An gudanar da kur'ani da tarjamarsa cikin harshen Sweden tare da hadin gwiwar ma'aikatar harkokin wajen Kuwait.

Ya kara da cewa: Ya kamata a rarraba wadannan kur'ani a kasar Sweden, kuma manufarsa ita ce jaddada al'adun hakuri a Musulunci, yada dabi'u da ka'idojin Musulunci, da kyakkyawar rayuwa a tsakanin dukkan bil'adama a yanayi mai cike da soyayya, hakuri da zaman lafiya. , da kuma kawar da kiyayya, tsatsauran ra'ayi da son zuciya.

Al-Dihani ya kuma ci gaba da cewa: Wannan aiki ba sabon abu ba ne a kasar Kuwait, kuma kasar ta ba da kulawa ta musamman ga kur'ani da kuma buga ilmummukan kur'ani tun a baya.

Idan dai ba a manta ba, wani dan kasar Iraki mai suna "Salvan Momika" ya kona kur'ani mai tsarki a gaban babban masallacin birnin Stockholm a lokacin da ake gudanar da bukukuwan sallar Idi a birnin Stockholm fadar mulkin kasar Sweden. Wannan danyen aikin dai ya fuskanci tofin Allah tsine ga kasashen Larabawa da Musulunci da kuma na duniya baki daya, sannan Iraki ta bukaci a mika Momika domin yi masa shari'a.

 

4154213

 

captcha