Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, a safiyar yau Lahadi ne al’ummar Palastinawa na zirin Gaza suka gudanar da bukukuwan mayar da martani ga Iran dangane da harin da aka kai kan karamin ofishin jakadancin Iran da ke birnin Damascus.
Jajirtattun sojojin sama na dakarun kare juyin juya halin Musulunci a safiyar yau Lahadi, tare da sauran dakarun wannan kungiya mai fafutukar neman sauyi da farin jini, da zummar hukunta haramtacciyar kasar Isra'ila da muggan laifukanta, inda aka kaddamar da farmakin ramuwar gayya na "Alkawari na Gaskiya". Inda da dama daga cikin makamai masu linzami da jirage marasa matuka sun yi luguden wuta a cikin yankunan da aka mamaye tare da auna filin jirgin saman sojojin mamaya a Naghab.